Ambaliya: Wani magidanci da ya’yansa biyu sun mutu a Abuja

0

Shugaban hukumar bada agajin gaggawa na babban birnin Tarayya ‘FEMA’ Idriss Abass ya sanar da mutuwar wani magidanci da ya’yansa uku sanadiyyar ambaliyar ruwa da akayi a unguwar Lokogoma a Abuja.

Ya fada wa manema labarai cewa hakan ya faru ne da safiyar Alhamis da karfe 7 zuwa 9 inda uba da ya’yansa biyu (namiji da namace) suka mutu a cikin ruwan.

Idriss Abass ya ce duk da ce wa mutanen unguwan sun yi ta hana wannan mutumi bin hanyar da motar sa, yayi musu kunnen uwar shegu.

Da yake ya zo da karewar kwana, shigan su ke da wuya ruwar ko ta hadiyesu sai da wasu yan unguwan suka shiga ruwan sannan suka tsamo gawawwakin su.

Bayan an gudanar da bincike akan mtumin, an gano cewa mazaunin unguwar Apo ne.

Yanzu dai an kai gawawwakin su asibitin Jabi.

Share.

game da Author