Kananan Hukumomin Dutsi, Mani da Ingawa sun samu ruwan sama mai karfin gaske, bayan an shafe sama da kwana goma ana rokon ruwa har a masallatan garin Dutsi, Mani da Ingawa. Majiya mai karfi ta ce ruwan sama ya goce har bayan karfe 11 na safe.
Ba a Karamar Hukumar Dutsi kadai aka yi rokon ruwa ba. An yi har a Kananan Hukumomin Mani da Ingawa. PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin yadda ake fama da karancin ruwan sama a wasu kananan hukumomin jihar Katsina. Ta kuma ruwaito yadda ake ci gaba da rokon ruwa.
Hakan kuwa ya faru ne a cikin watan Agusta, lokacin da ake ruwa marka-marka a wasu garuruwa har ya na yin ta’adin gidaje da dukiyoyi.