Abubuwa 7 da ke sa mutum yayi ta jin yunwa

0

Wasu likitoci sun gudanar da bincike kan wasu ababe da ke sa mutum jin yunwa ko da bai dade da cin abinci ba.

Binciken ya nuna cewa halin rayuwar mutum, yadda wasu ke cin abinci da irin abincin da wasu ke ci ke kawo yunwa da ko sun ci abinci baya dadewa a cikinsu.

Sakamakon bayanan ya shawarci mutane da su dinga kula da irin abinci da suke ci domin yawan biye wa ciki shi ke kawo kiba a jiki.

Gasu kamar haka:

1. Yawan cin abinci masu sinadarin cabonhydrates kamar biskit,buredi, lemun kwalba mai zaki musamman coke.

2. Rashin shan ruwa a lokacin da ya kamata.

3. Fushi ko kuma bacin rai.

4. Rashin samun isasshiyar barci da hutu.

5. Cin abinci da sauri ba tare da ana ci ana hutawa ba.

6. Rashin cin abinci dake dauke da sinadarin ‘Protein’ kamar su kifi, wake, kwai da sauransu.

7. Yawan jin yuwa wata sa’an alamomin wasu magunguna ne da wasu ke she musamman ma su cutar siga (Diabetes)

Share.

game da Author