Abinci 7 da ke kara karfin kwakwalwar yara

0

Wasu likitoci sun lissafo abincin da zai taimaka wajen kara karfin kwakwalwar yara kanana.

Sunce karancinsu na hana yara gane ko kuma fahimtar abin da ya kamata da wuri musamman wajen karatu.

Saboda hakan ne suke kira ga iyaye maza da mata da su tabbatar yaran su sun sami abinci kamar haka:

1. Cin dafaffen kwai.

2. Cin ganyayyaki da ake ci kamar su karas,alaiyaho, tumatur da sauran su.

3. Cin kifi.

4. Madara(musamman wanda aka rage kitsen da ke jikin shi) domin yana dauke da sinadarin ‘Vitamin B’ wanda ke taimakawa wajen bunkasa kwakwalwan yara.

5. Manan kasa ko kuma manan talotalon da aka cire fadan saboda fatan na kawo kiba.

6. Cin alkama da abincin da aka yi da alkama.

7. Cin kayayyakin lanbu kamar su lemu, kankana,ayaba da sauransu.

Share.

game da Author