Fadar Shugaban Kasa ta bayar da tabbacin cewa mulkin Shugaba Muhammadu Buhari ba zai yi wa kafafen yada labarai takunkumi ba.
Mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai, Femi Adeshina ne ya bayar da wannan tabbacin a ranar Alhamis, yayin da ya ke jawabi a taron shugabannin masu kafafen yada labarai na intanet, a otal din Ikeja da ke Lagos.
Adesina ya ce mulkin Buhari ya na nan a kan bakan sa na jaddada ‘yancin ‘yan jaridu da kafafen yada labarai, don haka babu ruwan sa da tunanin kakaba wa kafafen yada labarai takunkumi.
Sai dai kuma ya yi nuni da cewa gwamnatin Muhammadu Buhari na son ganin kafafen yada labarai na tafiya a kan tsarin da ya dace tare da kiyaye ka’idojin aiki ta hanyar yin sukar da ta dace, ba wai kowane kwaram da hama ya rika yayata kage, son rai da batutuwan da ka iya haddasa fitintinu ba.
Kakakin na Shugaban Kasa ya kuma shaida wa mahalarta taron cewa, tun farkon kafa wannan kungiya, shi mamba ne a cikin ta, ya na mai karawa da cewa mambobin kungiyar mutane ne masu kima da mutunci a fannin aikin jarida.
“Na shiga cikin wannan kungiya ne saboda na amince da cewa ayyukan ta a kan hanyar aikin jarida madaidaiciya su ke. Shi ya sa tun da farko na ke cikin ta.” Inji Adesina.
A na sa jawabin, shugaban kungiyar mai barin gado, Musikilu Mojeed, ya bayar da tarihin kungiyar inda ya ce kungiyar a ko da yaushe ta na bin diddigin mambobin ta domin tabbatar da cewa ba a kauce a kan kyakkyawan tafarkin tsarin aikin jarida ba.
Ya yi tsinkayen cewa yawan kafafen yada labarai na intanet, wato online ya karu kwarai da gaske a cikin shekarun nan. Sai dai kuma ya nemi a kafa tsauraran sharuddan da sai an cika su tukunna sannan masu kafafen yada labaran na intanet za su zama mambobin kungiyar.
Mojeed, wanda shi ne babban editan PREMIUM TIMES,ya ce a shirye su ke su hada kai da gwamnati domin a tsaftace harkar, ya na mai karawa da cewa kuma a shirye su ke su fallasa bara-gurbin da duk ya bata wa kungiyar suna.
A karshe kuma ya ce ba za su taba yarda gwamanti ta kakaba musu takunkumi ta kowace irin siga ba.
Discussion about this post