A tsaftace ruwan sha don guje wa kamuwa da cututtuka

0

Hukumar kula da hana yaduwar cututtuka ta Najeriya NCDC ta shawarci gwamnatin tarayya da ta yawaita kira ga mutane da su tsaftace ruwan shan su don guje wa kamuwa da cutar kwalara, zazzabin taifo, Hepatitis E da makamantan su musamman yanzu da damina ya kankama.

Hukumar ta sanar da haka ne ganin yadda cutar Hepatitis E ta bullo a jihar Borno inda mutane 562 suka kamu da cutar a kananan hukumomi 10 dake jihar.

Hukumar ta shawarci mutane da su guji yin bahaya a fili musamman a wuraren da ake dibo ruwan sha domin hakan na daya daga cikin matsalolin dake kawo cutar.

Hukumar ta kuma shawarci sauran jihohin kasarnan da su yawaita wayar da kan mutane akan hanyoyin guje wa kamuwa da cutar sannan hukumar ta yi alkawarin ci gaba da hada karfi da karfe da jihohin domin ganin sun magance yaduwa da cutar ta keyi.

Share.

game da Author