A shirye mu ke mu fara kamo shugabannin kamfanoni 30 – ‘Yan sanda

0

Rundunar ‘yan sandan Najeriya, ta bada sanarwar cewa a shirye ta ke ta fara aiwatar da umarnin da Majalisar Dattawa ta bayar cewa a kamo dukkan shugabannin kamfanonin da ke da hannu wajen janyo wa Nijeriya asarar kudaden haraji a tashoshin jiragen ruwa, har na yawan naira tiriliyan 30.

A ranar Larabar da ta gabata dai ne majalisar dattawa ta bayar da wannan umarni, saboda zargin da ake yi musu na haifar da asarar kudin shiga har na wadannan zunzurutun kudade.

An bada wannan sanarwa ne bayan jami’an kamfanonin duk sun ki amsa gayyatar da hadadden kwamitin kwastan, haraji da kuma harkokin sufurin tashoshin jiragen ruwa ya yi musu. An kuma ce an sha tunatar da su batun gayyatar, amma duk su na yin biris.

Kakakin rundunar ‘yan sanda Jimoh Moshood ya shaida wa Premium Times a ranar Litinin cewa ‘yan sanda na sane da umarnin, kuma a shirye su ke su fara kaddamar wa wadanda aka ce su kamo.

Kamfanonin 30 da ake neman shugabannin na su, sun hada da:

1. Globacom na Mike Adenuga.
2. Crown Flour Mills.
3. British American Tobacco.
4. CCECC
5. Dana Group
6. Olam Int. Ltd.
7. Hong Xing Steel Co. Ltd.
8. Visafone
9. African Wire 10. Star Comments and Allied Ltd.
11. Aarti.
CEO – Sohan Lal Mittal.
12. Abyem-Diva Int. Ltd CEO
13. Gagasel International
14.Friesland Campina
15. Etco Nig. – Etco (Nigeria) Limited
16. Edic Chemicals and Allied.

17. De United Foods
18. Don Climax Group
19. Skill G Nigeria Limited
20. Premium Seafood.
21. La Rauf Nig. Ltd
22. Standard Metallurgical Co. Ltd
23. Kam Industries
24. IBG Investment Limited
25. Orazulike Trading Co. Ltd.
26. Popular Foods
27. A-Kelnal Integrated & Logistics Services.
28. African Industries
29. African Tiles & Ceramics
30. ZTE Nigeria Limited.

Share.

game da Author