Kungiyar Matasan Arewa mai suna ‘Arewa Youth Assembly’ (AYA) ta gudanar da zanga-zangan lumana ranar Laraba domin tunatar da gwamnatin tarayya kan bukatar su na a kama goran kungiyar IPOB masu fafutikar neman kafa kasar Biafra Nnamdi Kanu ko su hana aiyukan gwamnati a kasar.
Masu zanga-zangar sun yi tattaki ne daga matattara na ‘Unity Fountain’ zuwa fadan shugaban kasa.
Idan ba a manta ba ranar 27 ga watan Yuli ne kungiyar AYA ta ba mukaddashin shugaban kasa Yemi Osinbajo Wa’adin kwanaki 10 da ya umurci jami’an tsaro su kama jagoran kungiyar IPOB Nnamdi Kanu ko su hana aiyukan gwamnati a kasar.
Kungiyar ta jaddada wa gwamnatin tarayya kan matsalolin da ka iya faruwa idan hakan bai yiwu ba.
Kungiyar ta ce dalilin yin hakan shine ganin cewa Nnamdi Kanu ya karya sharuddan da kotu ta gindaya masa a belinsa.
Daya daga cikin ‘yan kungiyar Mohammed Salihu ya fada wa gidan jaridan PREMIUM TIMES cewa kungiyar ba za ta yi amai ta lashe ba kan wa’adin da suka ba gwamnatin tarayya.