A gyara asibitocin mu kamar yadda na kasashen waje suke – kungiyar NMA

0

Shugaban kungiyar likitocin Najeriya ‘NMA’ Mike Ogirima ya yi kira ga shugaban kasa Buhari da ya gyara asibitocin kasan kamar yadda na kasashen waje suke.

Ya yi wannan kira ranar Litini bayan kammala taron da kungiyar tayi Kaduna.

Mike Ogirima ya ce gyara asibitocin kasa zai taimaka wajen rage kashe kudade da wasu ‘yan Najeriya ke yi wajen tafiya kasashen waje neman magani.

“Muna kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya yi amfani da abin da ya gani a asibitin da ya tafi don gyara na Najeriya.”

Share.

game da Author