A fara hukunta masu yada kalaman kiyayya da labaran karya -Sarkin Musulmi

0

Mai Alfarma Sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar, ya bayyana cewa sarakunan gargajiya na goyon bayan dokar yada kalaman kiyayya da labaran karya da Gwamnatin Tarayya za ta sa wa hannu.

Sultan ya bayyana haka ne a Abuja ranar Alhamis a wurin wata lacca domin cikar Hukumar Kula da Kafafen Yada Labarai ta Kasa, NBC, cikarta shekaru 25 da kafuwa.

Sarkin Musulmi ya kara da cewa irin wadannan mahaddasa fitina da masu kitsa karairayi su na watsawa, dukkan su ya dace a saka su cikin rukunin ta’addanci.

Ya kara da cewa masarautun gargajiya na da muhimmiyar rawar takawa kuma su na goyon bayan kalamin da Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osibanjo ya yi cewa, “da masu yada kalaman kiyayya da masu kitsa labaran karya, duk ba za mu yi sakaci su haddasa masa bala’i a kasar nan ba.

Sultan ya ce ko shi an gillara karya aka danganta da shi a ranar Labarar da ta gabata, inda aka ruwaito cewa wai ya ce, “ba na goyon bayan sake sabon layen tsarin Najeriya.”

Shi ma tsohon shugaban jami’an tsaron tsohon Shugaban Kasa, Janar Sani Abacha, ya y i jawabi a wurin. Hamza Al-mustafa, ya goyi bayan matakan da gwamanti za ta bi ta dakile kalaman kiyayya da labaran shifcin-gizo da shi ma ya ce duk su na kara ruruwa sosai a kasar nan.

Share.

game da Author