Yadda mahara su ka bude mana wuta a coci, cewar wadanda su ka tsira

0

Tabbatattun bayanai sun nuna cewa wani mai dauke da bindiga ne shi kadai ya shiga cikin cocin Saint Catholic Church na garin Ozubulu a jihar Anambara, inda ya bude wuta har sai da harsashen sa ya kare, kuma ya sake yi wa bindigar sa duri, ya ci gaba da zabarin wuta.

Haka dai wani wanda ke da rabon kwana a gaba, ya bayyana wa PREMIUM TIMES yadda aka yi harbin a kan idon sa.

Charles Justice, wanda ya kai abokan sa Asibitin Koyarwa na Nnamdi Azikwre, ya bayyana cewa an bude musu wuta ne da jijjifin safiyar Lahadi, wajen 6 na safe, bayan sun kammala addu’a.

”Yawancin wadanda su ka rasa rayukan su yara ne kanana da kuma dattawa. Domin na san akalla kananan yara uku da su ka mutu, wadanda ba su cika shekaru biyar-biyar ba.” Haka Justice ya shaida wa PREMIUM TIMES.

Ya kara da cewa wasu da su ka samu munanan raunuka su uku, sun mutu a cikin asaibiti. Wannnan rahoton wani likita ma ya tabbatar da shi, amma ya ce kada PREMIUM TIMES ta ambaci sunan sa.

Har ila yau, PREMIUM TIMES ta samu labarin cewa wasu mutane 18 da su ka samu raunuka na kwance a asibiti ana duba su, yayin da an yi wa wasu shida tiyata daga mummunan raunuka da aka ji musu.

Akalla mutane sha daya ne maharan su ka kashe nan take, a lokacin da su ka bude wuta a cikin cocin yayin da ake gunanar da ibada da sanyin safiyar Lahadi.

’Yan sanda sun ce a binciken farko da su ka gudanar, ya tabbatar da cewa harin musabbabi ne daga rashin-jituwa tsakanin wasu ‘yan asalin garin, mazauna wata kasar waje.

“Daya daga cikin su ne ma ya gina cocin da aka shiga aka bude wuta. Amma ba harin Boko Haram ko Fulani makiyaya ba ne.” Haka Kwamishinan ‘Yan sandan jihar Garba Umar ya bayyana.

Share.

game da Author