Kwamishinan kiwon lafiya na jihar Filato Kuden Deyin ya ce wannan itace karo na hudu da cutar zazzabin Lassa ta sake bullowa a jihar.
Ya ce mutane hudu sun kamu da cutar wanda uku daga cikinsu na samun kula a babbar asibitin garin Jos sannan mutum daya ya mutu.
Kuden Deyin ya shawarci mutanen jihar da su tsaftace muhalinsu da abincin da za su ci sannan su tabbatar abincinsu baya kusa ko kuma inda bera suke.