Mukaddashin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, ya ce gwamnatin tarayya za ta maida hankali wajen ganin ta bunkasa aikin hako ma’adanai dake Arewacin Najeriya domin bunkasar arziki kasa.
Osinbajo ya ce gwamnati za ta maida hankali domin kara bunkasa noma da aikin ma’adanai dake jahohin Arewa.
Da yake jawabi da ya kai ziyarar aiki jihar Zamfara cikin wannan makon, Osinbajo ya bayyana cewa Allah ya albarkanci Najeriya da kasar noma da ma’adanai musamman a Arewa.
Ya ce gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari tana da aniyar ganin an samu yaduwar arziki a ko’ina a Najeriya ta hanyar wanzar da zaman lafiya da wadata tsakanin mutane.
A cewar Osinbajo “akwai kasar noma da ma’adanai sosai a wurare kamar Zamfara kuma za mu yi aiki tukuru mu tabbatar an bunkasa wannan arzikin”.
Ya ce Najeriya tana da dukkanin abinda kasa ke bukata ta samu ci gaba, amma ci gaban ba zai samu ba sai mutane sun zauna lafiya a tsakaninsu. A don haka Osinbajo ya ce gwamnatin Buhari na matukar kokarin ganin an samu hadin kan ‘yan kasa da kuma wanzuwar zaman lafiya a ko’ina domin sai da zaman lafiya ne arziki zai yadu.
Mai rikon mukamin shugaban kasar ya kuma isar da sakon gaisuwar shugaba Buhari, wanda ya ziyarta a makon da ya gabata, ga al’ummar jihar Zamfara.