Gwamnatin Najeriya za ta karbi bakuntan taron ma’aikatan jinya da unguwar zoma na yankin yammacin Afrika wanda za a yi daga ranar daya zuwa takwas ga watan Yuni.
Ministan kiwon lafiya Isaac Adewole ya sanar da hakan ga manema labarai inda ya ce taron itace karo na 37.
Za a tattauna ne a kan abubuwan da ya shafi kiwon lafiya da ayyukan ma’aikatan jinya da unguwar Zoma.
Isaac Adewole ya ce an fara yin irin wannan taro ne tun a shekarar 1981 domin bunkasa ilimin aikin kula da marasa lafiya a yankin yammacin Afrika sannan kuma da karfafa yin bincike a fannin aikin kula da marasa lafiya.
Daga karshe ministan ya ce kasashen yankin yammacin Afrika kamar Gambia, Ghana, Liberia, Nigeria, Sierra-Leone da Jamhuriyan kasar Benin za su halarci wannan taro.