Gwamnatin Kaduna ta sanar da tantance mutane 230 domin zama hakimai da dagatai a yankuna 77 na jihar.
Kakakin Gwamna Nasir El-Rufai , Samuel Aruwan ne ya fitar da wanna sanarwa yau a garin Kaduna.
Gwamnatin jihar Kaduna ta rusa masarautun jihar sama da 4000 in da ta dawo da yankuna 77 kamar yadda suke kafin zuwan gwamnatin Ahmed Makrfi da ya kirkirosu a 2001.
Aruwan ya ce gwamnati ta dauki matakin ne bayan majalisar zartarwa na jihar ya amince da rahoton wani kwamiti da aka nada domin duba yadda hakimai da dagatai ke gudanar da mulkinsu a gundumominsu.
“Taron da majalisar zartarwa ta yi ranar 24 ga watan Afrilu ya gano cewa ba a bi wasu ka’idojin da ya kamata ba wajen kara masarautu daga 77 zuwa 390 ba a lokacin wancan gwamnati da tayi hakan. Wannan an yi shi ne don cimma burin wasu a siysance in da suka bar kananan hukumominmu da tirka tirkar yadda zasu biya masarautu 313 da aka kirkiro in da hakan ya rage kimar hakimar da hakimai suke dashi a idanuwar mutane.”
Yanzu dai za a tantance mutane 230 da aka karbi takardunsu na neman zama hakimai da dagatai a yankuna da gundumomin jihar.
Discussion about this post