A ci gaba da yi wa kundin tsarin mulkin kasa garanbawul da ya gudana a majalisa yau, sanatoci sun amince da wasu ababe guda biyar masu mahimmanci da suke ganin yana neman a gyara.
Gasu:
1 – Majalisar ta amince a dinga zabar wanda za a nada Ministan Abuja daga Yankunan babban birnin tarayyar 6 mai makon a nada ko waye.
2 – Hukumar Zabe ta kasa ta dinga shirya da zaben kananan hukumomi, maimakon gwamnoni a jihohi.
3 – Kudaden kananan hukumomi ya dinga zuwa daga asusun gwamnatin tarayya zuwa ga kananan hukumomin mai makon Jihohi.
4 – Shugaban Kasa da gwamnoni su mika sunayen ministoci da kwamishinonin da zasu yi aiki dasu kwanaki 30 bayan an rantsar dasu.
5 – A raba ofishin ministan shari’a dana Antoni Janar din kasa, haka ma a jiha.