Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, ta bayyana cewa ba za ta kauce wa dukkan wasu ka’idoji da kotu ta tanadar wajen yi wa Sanata Dino Melaye kiranye ba.
Daraktan Yada Labaran hukumar Oluwole Osaze-uzzi ne ya bayyana wa Premium Times haka a yayin wata tattaunawar neman fatawa da aka yi da shi ta wayar tarho.
Ya ce hukumar zabe ta samu kwafin takardar da Babbar Kotun Tarayya ta Abuja ta aika mata, dangane da batun yi wa Dino Melaye kiranye.
Ya ce sai sun zauna sun yi nazarin kwafin takardar sannan ne za su iya bayyana mataki na gaba da za su iya dauka dangane da batun kiranyen da ake shirin yi wa Melaye, wanda Sanata ne mai wakiltar shiyyar jihar Kogi ta Yamma.
Dino Melaye dai ya garzaya kotu ne inda ya nemi a dakatar da batun kiranyen da ake shirin yi masa.
Bayan duba takardun da kotu ta aika musu da shi, Hukumar ta amince ta bi dokar kotun zuwa lokacin da aka warware takaddamar da aka shigar gabanta domin ta warware.
Discussion about this post