Akalla mutane takwas ne su ka rasa rayukan su a ranar Litinin din nan, yayain da wata ‘yar kunar-bakin-wake ta tashi bam a cikin masallaci, a tsakiyar masallata a Maduguri. Hada dai jami’an tsaro da kuma shaidun gani-da-ido su ka bayyana.
‘Yar kunar-bakin-waken dai ta tashi bam din bayan da jami’an tsaro su ka kure mata gudu, inda ta afka a cikin masallaci. Rahotanni sun ce wasu mutane 13 sun samu munanan raunuka.
Premium Times Hausa ta samu tabbacin cewa wasu mutane hudu kuma sun rasa ran su a wani harin daban da wannan yarinya ta kai a masallaci. Majiyar ta ce masallacin da aka kai wa harin ya na kan titin Zannari, a kan hanyar Maiduguri zuwa Dikwa.