Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya ce yanzu fa ‘yan Najeriya na matukar bukatar PDP ta dawo mulki a 2019.
Jonathan ya fadi haka ne da ya jagoranci tawagar wasu ‘ya’yan jam’iyyar kwarya-kwaryar taro da jam’iyyar ta yi a hedikwatar ta dake Abuja.
Jonathan ya ce akwai ‘ya’yan jam’iyyar da suka canza sheka a 2015 inda suke shirin dawo.
Yayi kira ga ‘ya’yan jam’iyyar da su hada kansu sannan su mai da hankalinsu wajen yi wa jam’iyyar aiki domin ganin ta samu nasara a zabukan 2019.
Discussion about this post