Yadda aka kama Saminu Turaki

0

Bayan shekaru kusan uku Kenan da kotu ta bada umarnin a kama tsohon gwamnan jihar Jigawa Saminu Turaki abin kamar almara sai gashi yau jami’an hukumar EFCC sun tasa keyarsa a wajen taron kaddamar da wata littafi na marigayi Maimalari a Abuja.

Duk da cewa ana neman sa kuma kuto ta ce a kama shi tun shekarar 2014, hakan bai hana Saminu yin abinda da ya ga dama ba wajen halartar taruka da duk wani taro da aka gaiyace shi.

Jiya ma Saminu ya halarci taron kungiyar tsofaffin ministocin jam’iyyar PDP inda bayan kammala taron ya zanta da manema labarai.

Yau kuwa halartar taron nasa ke da wuya sai jami’an hukumar tsaro na SSS da EFCC suka tarkatashi zuwa ofishin EFCC.

Dama can ana tuhumar Saminu da wawushe kudin jihar Jigawa lokacin da yake gwamnan jihar daga 1999 zuwa 2007.

Share.

game da Author