Wulakanci da cin fuskar da Sultan ya ke yi wa asalina da zuri’a ta ce yasa na ajiye sarautar Magajin Gari – Danbaba

1

Kamar yadda Hausawa kan ce ‘abu kamar wasa karamar Magana ta zama babba’, shine ya faru a fadar sarkin musulmi Abubakar a Sokoto in da tun anayi a boye abin yanzu ya fito fili kowa ya sani.

Jikan marigayi sardaunan Sokoto Ahmadu Bello, Hassan Danbaba wanda shine Magajin Garin Sokoto ya fito karara ya na zargi Sarkin Musulmi Saad Abubakar da neman hanyar da zai sa a Kulle shi a gidan yari.

Duk da cewa ya ajiye sarautar Magajin Garin Sokoto da yake rike da ita shekaru 20 kenan saboda rashin jituwa da ke tsakaninsa da sarkin Musulmin, Danbaba ya ce ya ce dole ya sanar wa duniya abinda ke tsakaninsa da Sultan Abubakar saboda kowa ya sani cewa idan wani abu ya faru da shi a tambayi sarkin Musulmin.

Danbaba ya karyata rade-radin da ake ta yadawa wai ya nemi sarkin Musulmin ya sa baki a wasu sama da fadi da ake zargi da hadin bakin wasu kamfanoninsa a wasu kwangiloli da akayi da kuma maganar kudaden Paris Club da shi ma ake zarginsa akai.

Danbaba ya ce a sanin Sarkin Musulmi Saad Abubakar da yayi ya san cewa yana ma komai kudi ne a masarautar, kuma ya san cinikinsa wanda da hakan yake so da ya biya cinikin don ya sa masa baki akai.

Ya ce tun a da bai nemin taimakon sa ba sai ba sai yanzu da ya san ya fi karfin yin haka.

“Game da sauka da nayi daga sarautar Magajin Garin Sokoto kuma. Lallai na na yi haka ne da kai na saboda ba zan iya daukar irin wulakanci da cin fuska da Sarkin Musulmi ya ke yi wa asalina da zuri’a ta ba.

Share.

game da Author