Jahed Choudhury dai matashi dan asalin kasar Bangladesh ne wanda ya ke zaune a kasar Britaniya.
Duk da cewa Iyayensa sun yi iya kokarinsu wajen nuna masa illar abinda yake so tun a baya, hakan bai yiwu ba don har aikin Hajji sun tura shi ko zai canza ra’ayinsa amma Ina.
Bayan ya gaji da muzguna masa da akeyi ya yi kokarin kashe kansa.
Wata rana ya tafi bakin teku ya na zaune ya na ta kuka sai wani mutum mai suna Sean Mogan ya ganshi yana kuka. Da yayi kokarin ya lallasheshi sai ya yi masa bayanin abin da ya sa shi kuka.
Daga nan ne fa suka kulla soyayya a tsakaninsu inda tuni sun yi aure ma.
“ Babu abin da ya ke damu na tun bayan haka. Ina jin dadin rayuwa ta kuma wannan zai zama darasi ga mutane musamman wadanda suke ganin mutum ba zai ta ba zama yana harka da jinsin sa ba kuma yana musululci.
Dalilin wannan hanya da ya dauka ya zama abin kyama ga iyayensa da yanuwansa. Kamar yadda Choudhury ya fadi.
Ya ce yanzu ya na cikin farinciki domin za su hada wata gagarumar biki a kasar Ingila sannan kuma bayan haka zasu tafi kasar Spain domin ci gaba da holewa.
Gidan jaridar Telegraph ne ta ruwaito wannan labari.