Wani dan aji daya a makarantar Sakandare ya dirka wa yar ajinsu ciki

2

Uwar wata yarinya yar aji dayan wani makarantar Sakandare dake Abuja mai suna Rhoda Joshua ta roki kotun sauraren kara dake Karu Abuja da ta tilasta ma saurayin ‘yarta mai suna John ya biya ‘yarta naira 800,000 saboda ciki da yayi mata.

Rhoda Joshua ta fada a kotun cewa ta gano cewa ‘yar ta dake aji daya a makarantan sakandare na taba harka da wannan saurayi nata ne tun a shekarar bara amma bata san abin ya wuce saninta ba.

“A matsayi na ta mahaifiyar ta na yi kokarin nuna mata mahimmancin sa kai a karatunta ta rabu da wannan soyayya da take yi da Jon amma abin ashe ba haka aba.”

Ko da ya ke yarinyar ta sanar wa uwar cewa shi John din yayi alkawarin aurenta wanda tunda ya gano tana da ciki ya waske abinsa. shi bai nemi inda take ba ballantana ya san halin da take ciki. Sannan yaki ya bata kudin da zata kula da dan na su.

John ya amsa laifinsa amma duk da ya fadi a kotun cewa lallai shine ya yi mata ciki sai dai ba zai iya aurenta ba yanzu saboda shima yarone dan makaranta. Ya roki kotu ta laminta masa ya ding aba yarinyar wani abu domin ci gaba da duba dan nasu.

Alkalin Kotun Abdullahi Baba ya tura sharia’ar zuwa kotun Kwastamari dake Abuja.

Share.

game da Author