Rikicin da ya nemi ya tarwatsa fadar Sarkin Musulmi tsakanin jikan marigayi Sardaunan Sokoto Ahmadu Bello, Magajin Gari Hassan Danbaba da Sarkin Musulmi Abubakar Saad ya kawo karshe domin an yi sulhu.
Hassan Danbaba ya sauka daga sarautar Magajin Gari bayan sabani da ya samu da fadar Sarkin musulmi kan neman nada Inuwa AbdulKadir sarautar marafan Sokoto da take kokarin yi.
Hassan ya kalubalanci cancantar Inuwa AbdulKadir wanda sarautar mahaifinsa ne ya rike kafin marigayi Umaru Shinkafi.
Hassan Danbaba ya ce Inuwa AbdulKadir ba da bane bawa ne domin kakansa siyansa akayi.
Bayan neman sulhu da Masarautar ta nemi yi tsananin shi Inuwa da Magajin Gari, ta nemi Hassan ya sa hannu a wata takardar da Inuwa ya rubuto don neman sulhu, Magajin gari yaki amincewa da haka inda ya ce bai gamsu da abinda wasikar ta kunsa ba.
Dalilin haka Hassan ya fice da ga fadar sarki sannan ya ce a ajiye sarautar Magajin Gari da yake kai, sannan ya aiko da mota da kuma abubuwan da ke mallakin Masarautar Sokoto ne.
Daga baya Masarautar ta maida masa da su.
Sarkin Kano Muhammadu Sanusi da Sarkin Gwandu sun sasanta Sultan Abubakar da Magajin Gari Hassan Danbaba inda suka bukaci Magajin Gari da ya roki Sultan a matsayinsa na uba. Hassan yayi hakan kuma Sultan Abubakar ya amince.
Discussion about this post