Alhaji Shittu Mohammed shi ne Shugaban Jam’iyyar Advanced Peoples Democratic Allience, wato APDA na kasa baki daya.
Jam’iyyar na daya daga cikin jam’iyyun da aka yi wa rajista baya-bayan nan. A cikin wannan Tattaunawa Ta Musamman da yayi da PREMIUM TIMES HAUSA ranar Litinin a ofishin sa da ke Wuse II, Abuja, za a ji manufar jam’iyyar, kudirorin ta da kuma alkiblar da ta ke so dimokradiyya ta fuskanta.
PTimes Hausa: A matsayin jam’iyyar ku APDA, wane irin tanadi ta yi wa ‘yan Nijeriya, ganin cewa sabuwar jam’iyya ce?
Shittu: Jam’iyyar APDA ta kunshi jama’a masu ra’ayoyi iri daya. Sun zauna sun yi nazarin kalubalen da ake fuskantar kasar nan. Sai su ka gano cewa babu wasu matsalolin da su ka wuce na shugabanci, kama-karya da kuma rashin gina ginshiki mai dorewa a kasar nan.
Mun yi amanna da cewa a matsayin mu na dunkulalliyar al’umma, dole ne mu tashi mu samar wa kan mu mafita domin dorewar dimokradiyya mai inganci a kasar nan. Mu na da yakinin cewa tilas sai mun kara ciccibar dimokradiyya mun kai ta a gaban al’umma domin su shigo a yi da su, ba su na can gefe a na yi su na kallo ba.
Ka ga a matsayin mu na jam’iyyar, mun shigo da tsarin biyan kudi ta intanet, haka ma yin rijista da jam’iyya duk ta intanet za a iya yi a saukake. Mun nuna cewa bai yiwuwa ka zauna a Abuja ko Lagos kawai daga can ka ce ka na so ka zama shugaban kasa. Sai ka je asalin mazabar ka. Sannan kuma za mu kawo tsari na wakilcin akwatu a zaben fidda-gwani, ta yadda dan takara zai ma iya zama wakilin jam’iyyar APDA a zaben shugaban kasa ko da ya samu kudri’a 37 kacal.
A taikaice dai a nan shi ne, duk yawan kuri’un da ka samu a kowace jiha, to a matsayin guda daya su ke, har sai ka samu kuri’a a kowace jiha tare da Abuja kenan. Ka ga kenan tilas sai dan takara ya karade kowace jiha domin a san shi ya san su, kuma ya gani sannan ya san irin halin da kowane yanki ke ciki. Idan ma su na shan wahala a titina, to za ka hau titin kai ma ka ji a jikin ka.
PTimes Hausa: Mene ne matsayin jam’iyyar ku a kan kiraye-kirayen da ake yi cewa a sake zaunawa a kasa tsarin Najeriya a faifai, a sake rabo?
Shittu: Ai mu akwai ma wannan tsari a cikin daftarin jam’iyyar mu. Mun yi imani da cewa Najeriya na bukatar a sake zama a duba yadda tsarin ta ya ke, mun kuma yarda da tsarin karkasa iko zuwa bangarori ko shiyya, ta yadda kowace shiyya za ta duba irin albarkatun kasar da ta ke da shi, ta kara inganta su domin kara inaganta tattalin arzikin kasa.
Yanzu ka tashi ka je jihar Bayelsa, ka ma manta da fetur da su ke da shi. Za ka ga katafaren filin noman shinkafa.
To ashe idan za a rika yi irin wannan, to zai taimaka wajen samar da aikin yi ga dimbin matasan da ke kukan rashin aiki.
Za mu rage yawan kwarara birane kamar Abuja da ake yi ana neman kwangiloli, ta hanyar samar da ababen yi a jihohi. Sannan tilas sai mun jefar da tsarin wannan dan-kasa ko wancan bako ne. Mu zama daya kawai a duk inda dan Nijeriaya ya ke da zama. To ka dan ji kadan daga cikin irin manufofin wannan jam’iyya ta mu.
PTimes Hausa: Amma fa ‘yan Nijeriya da dama na ganin kamar jam’iyyun da mu ke da su, sun yi waya sosai. Me ka ke gani a kan haka?
Shittu: Ya kamata ka fahimci cewa kafa jam’iyya akida ce. Akwai jam’iyyu kusan 170 a Amurka kadai. Amma kowace ta na da ta su akida, wasu ma akidar su ita ce kare hakkin dabbobi kawai. Wasu kuma kare muhalli daga barin sa ya gurbace. Wasun su kuma za ka same su a wasu kasashe, komin kankantar su, ba za ka iya cin zabe ba, sai ka hada kai da su. Ko ka manta ne lokacin zaben Obama? Ana saura kiris a a kayar da shi, sai jam’iyyar Tea Party ta yi maja da shi. To ka ga su wannan jam’iyyar akidar da kenan.
PTimes Hausa: An ga wasu mambobin jam’iyyar PDP da LP a lokacin kaddamar da ta ku jam’iyyar. Shin kun nemo su ne domin samun goyon bayan su?
Shittu: Kamar yadda ka sani, a baya na yi shugaban kwamitin jam’iyyu ma su bayar da shawara, don haka ina da kyakkawar alaka da kowace jam’iyya. Za ka iya cewa ka ga fuskokin wasu ‘yan PDP, LP, PPN, NNPP da sauran jiga-jigan jam’iyyu. Jama’a da dama sun halarci taron kaddamar da jam’iyyar mu domin su nuna mana cewa su na tare da mu.
PTimes Hausa: To ko jam’iyyar ku na da Kwamitin Amintattu kuwa?
Shittu: A yanzu dai abin da gare mu shi ne Kwamitin Zartaswa na Kasa da Shugabannin Zartaswa na Kasa. Mun bar batun kwamitin amintattun dattawa tukunna, saboda wadanda za su kasance a cikin wannan kasaitaccen kwamiti, mutane ne da su ka yi rawar gani wajen bauta wa kasar nan a fannoni daban-daban. Don haka ba gaggawa mu key i ba.
PTimes Hausa: A karshe ya karfin wannan jam’iyya ya ke? A wane sashe ko shiyyar kasar nan ku ka fi yawan mambobi?
Shittu: Mu na mambobi a duk fadin kasar nan. Kuma a yanzu mu na kan karbar dimbin jama’ar da ke ta yin rijistta da jam’iyyar mu, APDA ta intanet. Babu ruwan mu da cewa jam’iyyar mu ta waccan shiyya ce, ko mu ce babu ruwan mu da waccan shiyya. Ko’ina mu na bada muhimmanci, saboda mun hakkake da cewa ko dan wace kabila ne kai, to duk matsalar mu daya. Matsalar Ebira daya ce da matsalar Kanuri.
Don haka mu a APDA mun yi imani da cewa Nijeriya kasa daya ce dunkulalliya, babu ruwan mu da bangaranci ko shiyyanci. Mun yarda da cewa a samar da tsarin shugabanci ta hanyar zabe yadda za a inganta rayuwar al’umma.