TAMBAYA: Kwanaki nawa ne ya hallata ayi Kasaru?
AMSA: Alhamdu lillah, Tsira da Amincin Allah su tabbata ga shugabanmu Annabi
Muhammad SAW.
Ana yin Kasaru ne a tafiyar da takai tsawon Mil Arba’in da Takwas (48 Miles), matafiyi zai yi kasaru akan hanyar sa ta tafiya, ko tsawon kwanaki nawane kafin ya isa inda yake da nufin zuwa. Saidai idan matafiyin yana da niyar yin kwanaki Hudu (4), ko fiye da haka, kimanin kwatan kwacin da zai yi Salloli 20. To, da zarar ya isa masaukinsa
kasaru ta kare.
Amma indan tafiyar batakai kwana hudu ba (Salloli 20), to, matafiyin zai iya cigaba da kasarun sa har ya dawo garin sa.
A cikin Mazhaba ta Imamu Malik, ana yin Kasaru ne a tafiyar da takai tsawon Mil Arba’in da Takwas (48 Miles) ka wai. Kuma matafiyi zai ci gaba da kasarun sa matukar be yi niyar zama tsawon kwana hudu (4) ba, Ko da kuwa ya wuce kwana hudun, in dai tun alasi be yi kudirin yin kwana hudun ba.
A misali mutum ne ya yi tafiya don wata bukatar sa, kuma ya kudiri cewa duk sanda ya samu abinda ya ke nema, to, washe gari zai dawo gida. To, irin wannan mutumin zai yi tayin kasaru har tsawon kwanakin da ya yi yana jiran biyan bukatar sa.
An samu wasu kalilan daga cikin magabatan da suke ganin cewa za’a iya yin kasaru a tafiyar da takai mil 3, matukar dai a al’adance al’umar tana daukar irin wannan a matsayin tafiya. Sannan akwai wasu ‘yan kalilan da suke ganin cewa mutum zai iya yin kasaru tsawon kwana 10, ko 15 koma fiye. Amma fa wannan ra’ayi ne na ‘yan kalilan a cikin
magabata, wanda ya sabawa ra’ayin mafi yawan magabata. Kuma manyan malamai sun yi hani da daukar irin wannan ra’ayin. Allah she ne mafi sani.
TAMBAYA: Menene hukuncin hada Sallar matafiyin da zai yi kwana 5 a inda ya tafi. Wato Azahar da La’asar, sannan Magariba da Isha’i. ya hallata ko A’a?
AMSA: Alhamdu lillah, Tsira da Amincin Allah su tabbata ga shugabanmu Annabi Muhammad SAW.
Kasaru da Hada Sallah ga matafiye a cikin tafiya abu ne shaharrare a gurin Malamai, kuma babu sabani a wurin malamai, sannan yin hakan halal ne kuma sunnar Annabi (SAW) ne.
Amma fa idan matafiye ya yi niyar kwana Hudu, ko fiye da haka, Limaman mazhaba, Kamar Imam Malik, Imam Shafi’i, da Imam Ahmad sun ce zai yi kasaru kuma ya hada Sallah a cikin tafiyar sa ne kawai, lallai ne ya cika sallar sa kuma ya yi ta a lokacinta, da zarar ya isa masaukin sa (Wato ba zai yi kasaru ba kuma ba zai hada Sallah ba). Shi kuwa Imam Abu Hanifa ya ce isa inadan matafiyin ya yi niyyar kwana 15.
Wasu daga cikin magabata sun yi kasaru har tsawon wata shida, shekara daya, kai harma da shekara biyu.
Lallai masana sun tafi akan riko da abinda manyan Limamai suka tsaya akan sa, cewa bai dace musulmi ya yi kasaru ba idan yayi niyyar kwana 5 a cikin tafiyarsa kuma bai dace ya hada Sallah ba.
Sun bayyana cewa abinda Annabi ya yi na yin kasaru a tsawon kwana 15 ko 19, don ana cikin yakin fatahu Makkah da Khaibar ne. Kuma sojojin da suke bakin daga, sunada wannan dama na yin kasaru da hada Sallah a bakin daga, komai tsawon lokacin da za su yi. Kuma abinda wasu magabata sukayi na yin kasaru tsawon wata shida, shekara daya, ko
shekara biyu, kowanne nada dalilin yin hakan. Kenan yin haka a wajen mu bai dace da koyarwan magabata ba. Sai dai idan mutum ya sami kansa a cikin kwatan-kwacin halin da suka sami kansu a ciki.
Muna kira ga ma’aikata da ‘yan makaranta musu yin kasaru da hada salloli dogaro ga wadancan hujjoji da suji tsoron Allah su kyautata Ibadar su ga Allah, kamar yadda mafi yawan magabata suka karantar. Kar kabi ra’ayin ‘yan kalilan kabar ra’ayin masu rinjaye, domin Sallah ba abar wasaba ce.
Dan uwana mai girma, kar ka bari son sauki da arha ya tauye maka Zinariyar Ibadar ka ta Sallah. Sai kaga ma’aikaci ko dan makaranta yana yin kasaru da hada Sallah fiye da tsawon kwanakin da aka kayyade masa bayan ya san cewa zai zauna a garin da yake aiki ko makarantar su fiye da kwana hudu. To, zaka iya yin kasaru da hada Sallah ne kawai a
lokacin da kake tsakiyar tafiya, da zarar ka isa masauki, to kasaru da hada Sallah sun kare.
Allah she ne mafi sani.
Allah ka tsare mana Imanin mu da mutun cinmu, kuma ka karbi Ibadan mu. Amin.