Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya umurci jami’an tsaro da su binciki sannan su kamo wadanda suka kai hari a ofishin NUJ, Kaduna.
El-Rufai ya fadi haka ne a wata takarda da kakakinsa Samuel Aruwan ya saka wa hannu.
Sanata Shehu Sani da Suke Hunkuyi sun sha da kyar a wata hari da wasu da ba’a san ko suwa ye ba dauke da makamai suka kai musu a ofishin NUJ da ke Kaduna.
Shehu Sani da Sule Hunkuyi suna kokarin ganawa da ‘yan jarida ne a ofishin kan zargin gwamnan jihar da sukeyi na yin coge da musanya sunayen Daliget a zaben da akayi jiya a Kaduna.
Jam’iyyar APC a jihar ta musanta korafin sanatocin in da ta tabbatar da ingancin zaben Daliget din da akayi a jihar.
” An yi zaben daliget a Kaduna cikin kwanciyar hankali sannan kowa ya shaida cewa anyi zabe ne mai kyau kuma jam’iyya a jihar ta amince da wannan zabe.”