SHAWARA GA IYAYE: Ku yawaita shafawa ‘ya’yanku man kade da Zaitun – Likita Khadijat

0

Wata babban likitan yara kuma mazauniyar jihar Kwara Khadijat Ajadi ta shawarci uwaye da su dai na amfani da maganin kau da cutar fata ta hanyar hada shi da man da suke shafawa ‘ya’yansu don su kara haske a fatarsu.

Ta ce wasu uwayen na hada man shafawar ‘ya’yansu da maganin cutar fatar da ake kira ‘Funbact A ko kuma Skineal’ domin canza launin fatar ‘ya’yansu.

Khadijat Ajadi ta ce matsalolin da yaro kan fada ciki sun hada da bata fatarsa, kuraje , samun raunuka da wasu iin haka.

Ta ce ta yi wannan kira ne don ta jawo hankulan iyaye game da illolin da ke tattare da amfani da wadannan mai a jikin ‘ya’yansu domin bincike ya nuna cewa da yawa da ga cikinsu basu da masaniya kan illolin yin hakan.

Khadijat Ajadi ta ce uwaye za su iya amfani da manshafawa kamar su ‘Vaseline, mankade da sauran su domin suna gyara fatar yaro sannan ta yi kira ga iyaye da su kai ‘ya’yansu Asibiti idan suka kamu da cutar fata maimakon yin gaban kansu.

Share.

game da Author