Allah yayi wa mai martaba sarkin Tsafe Habibu Aliyu rasuwa.
Kwamishanan kananan hukumomi da harkokin masauratu na jihar Zamfara Muttaqa Rini ya sanar da haka yau a Gusau.
Sarki Habibu ya rasu ne a asibitin Usman Danfodio dake Sokoto.
Ya rasu ya na da shekaru 62 sannan ya bar mata 4, ‘yaya 25 da jikoki 62.
Ya gaji mahaifinsa ne a shekarar 1991.
An bizine marigayi Habibu Aliyu a garin tsafe yau Laraba.