Rikicin Manoma da Makiyaya: Sama da mutane 1,800 ne suka rasa rayukansu a jihar Benue

0

Gwamnan jihar Benue Samuel Ortom ya ce a cikin shekaru uku mutane 1,800 ne a  kananan hukumomi 12 suka rasa rayukansu dalilin rikicin makiyaya da manoma a jihar.

Ya fadi haka ne da yake zantawa da jami’in majalisar dinkin duniya UN Edward Kallon da ya ziyarci ofishinsa.
Ya kuma kara da cewa hukumar kula da bada tallafi na gaggawa a jihar da kungiyoyi masu zaman kansu sun gudanar da bincike inda suka gano cewa  mutane 750 sun sami raunuka dabam dabam a jikkunansu sannan mutane sama da 200 ne har yanzu ba a san inda suke ba.

Samuel Ortom ya ce iyalai 99,427 ne suka rasa muhallansu sanadiyyar wannan rikici inda hakan yasa akayi hasarar dokiyoyi masu yawa.

Daga karshe Edward Kallon ya tabbatar wa gwamnan cewa hukumar UN za ta goyi bayan gwamnatin jihar wajen kawar da wannan matsalar sannan kuma ya yi wa mutanen jihar da gwamnan jaje kan abubuwan da suka yi ta faruwa a jihar.

Share.

game da Author