RAHOTON MUSAMMAN: Saminu Turaki zai shafe kwanaki 77 tsare a hannun EFCC

0

Tsohon gwamnan Jihar Jigawa, Saminu Turaki, zai shafe kwanaki 77 ya na tsare a hannun EFCC, bayan kamun da hukumar ta yi masa a wurin taron kaddamar da littafi kan rayuwar Birgediya Zakariya Maimalari, wanda aka kaddamar ranar Talata, a Cibiyar Shehu Yar’Adua, Abuja.

Zai ci gaba da zama tsare a hannun EFCC har zuwa ranar 19 Ga Satumba, 2017, ranar da alkalin Babbar Kotun Tarayya ta Dutse ya aza ranar komawa domin ci gaba da tuhumar Turaki.

Tun ranar 3 Ga Mari, 2013 ake wasan-buya tsakanin Saminu da jami’an EFCC, bayan da alkali Sabi’u Yahuza ya bayar da umarni ga Sufeto Janar na ‘yan sandan kasar nan da EFCC cewa duk inda suka ga Turaki, su kamo shi, su gurfanar da shi a gaban sa.

Wannan umarni na alkali Yahuza ya biyo bayan irin yadda Turaki ya dade ya na kin halartar shari’ar sa da ya rika yi.

Turaki, wanda ya yi gwamna har tsawon shekaru takwas, tsakanin 1999 zuwa 2007, an gurfanar da shi a karon farko a kotu ne a ranar 13 Ga Mayu, 2007, a gaban Mai Shari’a Binta Murtala Nyako ta Babbar Kotun Tarayya, Abuja.

An caje shi da laifin yin tabargaza ta zunzurutun kudi har naira bilyan 36. Sai dai kuma an bayar da belin sa akan kudi naira milyan 100 ga ‘yan majalisar tarayya biyu, Hon. Bawa Bwari da Hon. Bashir Adamu a lokacin.

An maida shari’ar sa a kotun Dutse ta jihar Jigawa, bayan da ya kalubalanci kotun Abuja cewa ba ta da hurumin yi masa shari’a, domin dukkkan laifukan da ake tuhumar sa a kai, a Jigawa ne aka ce ya aikata su, ba a Abuja ba.

PREMIUM TIMES HAUSA na da hujjojin da su ka tabbatar da cewa, rabon da Turaki ya je kotu, tun cikin 2011 a lokacin da Mai Shari’a Yahaya ya karbi ragamar Babbar Kotun Tarayya ta Dutse, daga hannun Mai Shari’a Yunusa Nasiru, wanda aka tura zuwa sauraron kararrakin da suka jibinci zaben 2011 a lokacin.

A cikin 2012, Mai Shari’a Sabi’u Yahuza ya koma Babbar Kotun Tarayya ta Dutse, ya karbi aiki daga hannun alkali Yahaya. Premium Times Hausa na da kwararan shaidu tabbatattu da ke nuni da cewa daga ranar da alkali Yahuza ya kama aiki a kotun Dutse, cikin 2012, har yau Turaki bai gabatar da kan sa a kotun ba.

Ba mamaki wannan dalilin ne ya sa a wannan tsawon shekaru biyar aka rika daga sauraren shari’ar a ko da yaushe. Premium Times ta gano cewa an daga shari’ar sama da sau goma.

A kan haka ne Yahuza ya bayar da sammacen kamo Saminu a cikin 2013, inda tun daga lokacin ake ta kulli-kurciya da shi.

Zaman karshe da aka yi na ranar 30 Yuni, an aza ranar 19 Ga Satumba, 2017 ranar ci gaba da zama, duk kuwa da cewa Saminu ba zuwa kotun ya ke yi ba.

Premium Times Hausa ta tabbatar da cewa, shi kan sa jagoran lauyoyin EFCC, Rotimi Jacobs ya daina halartar kotun. Sai dai kuma a ranar zaman karshe na baya-bayan nan, wata lauya ta je kotun ta Dutse daga Kano.

Cikin 2014 da 2016, hukumar EFCC ta buga sanarwar cigiyar Saminu Turaki a duk inda ya ke. Ganin cewa bai cika zama Nijeriya ba ne ya sa hukumar har ta nemi taimakon ‘yan sanda na kasa-da-kasa, wato Inter Pol da su taimaka wajen cafke Turaki a kowace kasa a ka gan shi.

Sai dai kuma abin mamaki, hakan bai sa an kama shi ba, ta kai ma ana ganin sa ya na yawo a ko’ina cikin kasar nan.

Duk da cewa bai yi shelar ya koma jam’iyyar APC ba, amma an rika ganin sa a tarukan jam’iyyar APC a jihar Jigawa, inda ya rika taya gwamann yanzu Badaru Abubakar yakin neman zabe cikin 2014 da 2015.

Bayan nan, an rika ganin sa a wasu taruka na biki ko shagulgula. Da shi aka yi ruguntsumin bikin Zahra Buhari, ‘yar Shugaban Kasa a Daura, inda ya jera kwanaki biyu ya na zuwa Daura daga Kazaure.

Watannin baya kuma an nuno hotunan sa a jaridu da kuma talbijin yayin da ya halarci taro a kan jagoran APC, Bola Tinubu. Ranar Talatar da ta gabata kuma an nuna shi a talbijin ta AIT a wurin taron kaddamar da littafi, a Abuja, inda jami’an EFCC suka yi masa kofar-raggo bayan an tashi daga taron.

Ana tuhumar sa ne da caje –caje har 32, tare da wasu kamfanoni uku: INC Natural Resources Ltd., Arkel Construction Ltd., sai kuma wani kamfani mai suna Wildcat Construction Ltd.

Cikin takurdun caje-cajen da ake yi wa Turaki, wadanda a yanzu haka su na hannun Premium Times Hausa, akwai wani mai suna Ahmed Ibrahim Mohammed, wanda dukkan laifuka 32 da ake zargin Saminu da aikatawa, tare suka aikata, kamar yadda tuhumar ta nuna.

Sai dai kuma takardar gabatar da Saminu a kotu, wadda Premium Times ta samu, ta nuna cewa Ahmed ya cika wandon sa da iska, tun a wannan lokaci, 2007, ya gudu.

Cikin wani rubutu mai dauke da shafuka 20, wanda Saminu ya rubuta da biro, da hannun sa a ofishin EFCC, a cikin 2007, ya tabbatar da cewa ya san wadannan kamfanoni uku da ake tuhumar sa tare da su, amma kuma ya kafe a kan cewa shi ba ya bayar da kwangila a lokacin da ya ke gwamna.

“Sai da a wasu lokuta ina bayar da umarnin cewa ga kamfanin da za a bai wa kwangila, domin shi ne zai iya gudanar da ita.” Haka Turaki ya rubuta da hannun sa a shafi na takwas na rubutaccen bayanin da ya yi wa EFCC tun cikin 2007, bayan ya yi ikirari a rubuce cewa ba ya bayar da kwangila.

Takardar cajin Saminu a kotu mai lamba FHC/ABJ/CR/86/2007, wadda lauyan EFCC da ke sashen gabatar da kara na hukumar, mai suna Isa Bature Gafai ya sa mata hannu. Ta na dauke da bayanan yadda Saminu da wadancan kamfanoni uku tare da Ahmed Ibrahim Mohammed, wanda aka ce ya gudu, suka hada baki wajen wawure naira bilyan 32 na jihar jigawa a cikin shekara takwas.

PREMIUM TIMES HAUSA ta ga sunayen jami’an ‘yan sanda har 16 a cikin takardar karar, wadanda aka ce su ne za su bayar da shaidu dangane da yadda Saminu da sauran kamfanonin su ka yi harkalla. Sunan Ibrahim Magu ne na 13. Magu a yanzu shi ne shugaban hukumamar EFCC na riko.

Sai dai kuma wani bincike da Premium Times Hausa ta gudanar, ya nuna cewa a wannan tsawon shekaru goma da fara shari’ar Saminu Turaki, har yau ba a fara ma gabatar da shaidu a gaban alkali su na gabatar da na su shaidu ba.
Idan za a iya tunawa, Turaki ya taba bayyana cewa ya kafci wasu bilyoyin kudi daga baitulmalin jihar Jigawa ya bai wa Obasanjo gudummawa a lokacin yinkurin Tazarcen Obasanjo, wanda ba a yi nasara ba.

Har ila yau, idan ba a manta ba, jami’an EFCC sun taba yi wa Turaki samame a ranar 19 Ga Mayu, 2016 a gidan sa mai lamba 16, Titin Dennis Osadebey, cikin unguwar Asokoro, Abuja, amma ya zille, ba su damke shi ba.

A zaman yanzu ba Turaki kadai ba ne tsohon gwamnan da ake tuhuma daga jihar Jgawa. Shi ma wanda ya gaje shi, Sule Lamido, ya na gaban Mai Shari’a A.F.A Ademola na Babbar kotun Tarayya, Abuja, inda ake masa tuhumomi 44.

Premium Times Hausa ta mallaki kwafin takardar da aka gabatar da karar Lamido, kuma ta na bibiyar shari’ar. Daga bayanan da mu ka tattara, an tabbatar da cewa ba kamar Turaki ba, shi Lamido ya na halartar zamar shari’ar sa a duk lokacin da ranar gurfana a gaban alkali ta zo.

Premium Times Hausa ta tabbatar da cewa daga ranar 14 Ga Yuli, 2915 da aka fara shari’ar Lamido zuwa ranar 5 Ga Mayu, 2015, ya halarci zaman shari’ar sa sau 32, kuma an gabatar da masu shaidu har 18 a cikin wadannan shekaru biyu. Sabanin shari’ar Saminu da aka shafe shekaru 10 ba a fara gabatar da shaidu ba. An dai gurfanar da Lamido ne a karkashin takardar sammacen tuhuma mai lamba FHC/ABJ/329/2015.

Premium Times Hausa ta tabbatar da cewa alkali Yahuza na Kotun Tarayya da ke Dutse ba ya ma kasar nan a lokacin da aka cafke Turaki, sannan kuma alkalai za su fara hutun wata biyu tun daga ranar 10 Ga Yuli, 2017. Dalili kenan Turaki zai ci gaba da zama a hannnun EFCC, har sai bayan dawowar su daga hutu a ranar Litinin mai zuwa, 15 Ga Satumba, 2017, inda za a gurfanar da shi a ranar 19 Ga Satumba, 2017. Kenan zai shafe kwanaki 77 a hannun EFCC.

Karanta labarin a shafin mu na turanci: EXCLUSIVE: Ex-Jigawa governor, Saminu Turaki, to spend minimum 77 Days in detention

Share.

game da Author