Rahama Sadau ta shirga wa BBC Hausa Karya ne kan korar ta da MOPPAN ta yi – MOPPAN

12

Shahararriyar yar wasan finafinan Hausa, Rahama Sadau ta karyata cewa wai an kore ta a Kannywood.

Rahama ta fadi haka ne a wata hira da tayi da gidan jaridar BBC Hausa a Abuja.

Rahama ta shaida wa BBC cewa kamar yadda kowa ya gani a shafunan jaridu haka ita ma ta gani cewa wai an kore ta amma babu wanda ya aika mata da wasika kan haka.

” Ni fa babu wanda ya kore ni daga Kannywood. Har yanzun nan babu wanda ya aiko min da wata takarda da ke nuna cewa an sallame ni daga Kannywood.

“ An rage ganina a fina-finan ne saboda, kamar yadda na gaya maka, ina fitowa a fina-finan Nollywood da kuma gudanar da sauran al’amuran rayuwata.

“Amma yanzu zan koma yin fina-finan na Hausa gadan-gadan musamman ganin irin nasarar da fim dina na Rariya ya yi. Zan ci gaba da daukar nauyin fim baya ga fitowa a ciki da zan ci gaba da yi.” Kamar yadda Rahama ta ce a hirar ta da BBC Hausa.

Sai dai kuma hakan bai yi wa kungiyar MOPPAN dadi ba in da sakataren kungiyar Salisu Mohammed ya karyata hakan sannan ya ce ta fadi cewa ba a aika mata da wasikar korar na ta ba ne saboda neman suna kawai.

Salisu Mohammed , ya ce bai san dalilin da ya sa Rahama ta sanar wa BBC Hausa cewa wai bata sami sakon korarta da akayi a Kannywood ba.

“ Kamar yadda kowa ya sani ne cewa bayan ta aikata wannan laifi kungiyar MOPPAN ta kore ta daga Kannywood. Kuma bayan haka ita da kanta ta rubuto wasika inda ta yi bayani masu yawa sannan ta roki da a yafe mata. Bayan haka Kungiyoyi da mutane masoyanta sun yi ta bibiyan MOPPAN din duk don a yafe mata ta dawo harkar shirya finafinan hausa. To a haka ana cikin duba wadannan abubuwa ne kuma za ta ce wai ita bata ga wasikar korar da akayi mata ba sai a gidajen jaridu da shafunar yanar gizo ta gani.

Salisu yace Rahama dai tana neman kawai a ci gaba da biye mata ne amma abin da take fadi ba haka bane.

Share.

game da Author