Jam’iyyar APC ta sha kayi a zaben cike gurbin kujerar sanata sa akayi a jihar Osun a karshen makon da ya gabata.
Kanin marigayi Isiaka Adeleka na jam’iyyar PDP ne ya doke Shuaibu Hussein na jam’iyyar APC kamar yadda sakamakon zaben ya nuna.
Adeleke ya canza sheka da ga jam’iyyar APC zuwa PDP ana gobe za a gudanar da zaben fidda dan takara na jam’iyyar APC ganin cewa jam’iyyar ba za ta tsayar da shi ba.
Adeleke ya lashe zabe a kananan hukumomin 10 cikin 11.
Da yake zantawa da manema labarai bayan sanarwar nasarar da ya samu ya ce hakan yanzu za su hada kai domin tunkarar zaben gwamnan jihar da za a yi a shekara mai zuwa.
” Wannan ya nuna cewa jam’iyyar PDP ce zata samu nasara a zaben gwamnar jihar mai zuwa.
Discussion about this post