Gwanamtin jihar Kano ta karyata zargin da ake yi cewa wai ta biya kudin ruwa har na naira bilyan 1.3 daga bashin naira bilyan 9 da ta ciwo domin biyan albashin ma’aikatan jiha da na kananan hukumomi.
Kwamishinan kudi na jihar, Kabiru Dandago ne ya bayyana haka a lokacin da ya ke warware wa manema labarai zare da abawa inda ya ce naira milyan 10.7 kacal banki su ka caja.
“Ina jawo hankulan jama’a cewa ma’aikatar kudi ta ji wasu maganganu na kage marasa tushe da ake yayatawa a wasu kafafen yada labarai wai mun biya kudin ruwa mai yawan gaske.
Ya bayyana cewa bankuna biyu da su ka bayar da kudi, sun dora kudin ruwa na 14 bisa 100 da kuma 15 bisa 100 ne kawai, sabanin yadda ake ta yayatawa.
Kwamishinan ya kuma ce gwamnatin jihar Kano ta yi tunanin karbar lamunin ne domin a samu dama da sararin biyan ma’aikatan jiha da na kananan hukumomin jihar albashin su kafin 25 Ga Yuni, wato kafin ranar karamar sallah kenan.
Daga nan sai ya yi nuni da cewa kuma gwamantin jihar Kano ta biya dan adadin da aka dora mata kwanaki uku kacal bayan da kudin da gwamnatin tarayya ke bai wa jiha da kananan hukumomi su ka shigo.
“Idan mutum ya lissafa kashi 14 bisa 100 na naira bilyan 4.5 da kuma kashi 15 bisa 100 na naira milyan 5.5, gaba dayan adadin da za a gani kenan zai kama naira milyan 10.7 kacal. Inji kwamishinan.
Discussion about this post