LWata sabuwar Kungiyar Matasan Arewa mai suna Arewa Youth Assembly ta ba mukaddashin shugaban kasa Yemi Osinbajo Waadin kwanaki 10 da ya umurci jami’an tsaro su kama jagoran kungiyar IPOB masu fafutikar neman kafa kasar Biafra Nnamdi Kanu ko su hana aiyukan gwamnati a kasar.
A wata takarda ta musamman da Kungiyar ta fitar wanda kakakin kungiya majalisar matasan da Akawun ta Mohammed Salihu da Desmond Minakaro suka saka wa hannu ta ace ya kamata ace gwamnati ta dade da kama Nnamdi Kanu.
” Tun bayan bada belin sa da kotu tayi yake ta yin abin da ya ga dama a kasar nan. Babu wani abu daya da akace kada yayi da bai yi ba. Duk sharuddan da aka gindaya masa ya karya su kuma har ikirari ya ke yi cewa babu wanda ya isa ya kama shi.”
“Ganin haka ne ya sa muka ce ba za mu zura ido mu bari a na kallaonsa
Kawai babu abinda akayi akai ba.
” Saboda haka ne muka fito domin mu tunasar da mukaddashin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo domin gwamnati ta dau mataki akai.
“Idan har kwanaki 10 suka cika ba ace komai ba to zamu fito domin gudanar da zanga zanga sannan za mu dakatar da ayyukan gwamnati.
Majalisar matasan ta ce idan ya fi karfin gwamnati su bai fi karfin su ba.
Tun bayan kuto ta bada belin Kanu da gindaya masa wasu tsauraran sharudda da ta umurce shi dole ya bi Nnamdi Kanu ya yi musu kunnen Uwar shegu domin bayan haka ma har wadanda ba a hana shi ba kuma saba doka ce ya na aikatawa.
Discussion about this post