Wani magidanci a jihar Legas ya roki kotu ta warware auren sa da matarsa saboda neman kasheshi da take yi kullum rigima ya hada su.
Magidancin ya ce da zarar wani abu ya hada su sai matarsa ta kama masa marainansa tayi ta mutsitsikawa wanda hakan na saka shi cikin dimuwa da wahala.
Ya roki Kotu da ta warware kullin auren dake tsakaninsa da matarsa mai suna Obianuju.
Matar ta sa ta amince da abin da mijinta Chukwu ya nemi kotu tayi na raba aurensu domin ita ma ta gaji da shan duka.
“ Mijina yakan yi mini shegen duka inda har ciwo yakan ji mini. Duk Jikina ciwo ne kuma shine sanadiyya.
“ Ya taba lakada mini dukar da sai da ya cire mini hakori gashi kuma matsafi.”
Obianuju ta ce ta taba kama mijinta na yi mata tsafi cikin dare bai san ta tashi daga barci ba lokacin.
Alkalin Kotun dake sauraren karar ya daga ci gaba da haka zuwa watan gobe.