Wani likita kuma shugaban kungiyar ‘Health Sector Reform Coalition’mai suna Ben Anyene ya c cututtukar da ake fama da su musamman a cibiyoyin kiwon lafiya na daya daga ciki dalilan dake kawo mutuwar mata da yara kanana a Najeriya.
Ben ya fadi hakan ne a taron kadamar da wasu sabin ma’aikatan asusun GFF da aka yi a Abuja.
Ita dai wannan asusu na GFF na adashin kudade ne domin taimakawa mata masu ciki wajen haihuwa, kiwon lafiyar jarirai da yara (RMNCH) musamman a kasashen da suke da matsaloli irin hakan.
Ben Anyene ya kara da cewa hukumar WHO ta gano a binciken da ta gudanar a shekaran 2015 cewa adadin yawan matan dake mutuwa a Najeriya ya kai 814 sannan yara kanana ya kai 33.3 bisa 100.
Ya ce saboda hakan ne babbar bakin duniya tare da wasu kungiyoyin bada tallafi na kasashen duniya suka hada karfi da karfe domin tara kudaden da za a bukata domin ganin an rage mutuwan mata da yara kanana a Najeriya.
Daga karshe Ben Anyene ya shawarci sabobin ma’aikatan da su tabbatar sun yi aikin da zai taimaka wajen ganin an sami nasara akan haka.