Makiyaya 27, ‘yan gari 6 ne suka rasa rayukansu a rikicin Kaduna

0

Rundunan ‘yan sandar jihar Kaduna ta sanar da cewa akalla mutane 33 ne suka rasa rayukansu a riciki da ya barke tsakanin mazauna kauyukan karamar hukumar Kajuru da makiyayan yankin.

Da yake zantawa da manema labarai a Kaduna Kwamishinan ‘yan sandar jihar Agyole Abeh ya ce mazauna kauyukan Kajuru shida da makiyaya 27 ne suka rasa rayukansu a rikicin.

Agyole Abeh ya ce rikicin ya fara ne bayan an kai wa wani dan matashi makiyayi hari wanda bayan an kai shi asibiti ya rasu.

Bayan ganin hakan ya faru sai makiyayan dake kauyen suka kai wa mazaunan kauyen hari don daukar fansa inda suka kashe mutane shida a sanadiyyar harin.

” Daga nan ne fa sai ‘yan kauyen suka kai hare-hare rugagen fulanin da ke dazukan garuruwan suka kashe duk wanda suka gani. Kafin jami’an tsaro su iso sun gudu.”

“Mafi yawa cikin wadanda aka kashe matane da kananan yara. sannan wadanda suka sami rauni cikin Fulanin suna asibiti a na dubasu.”

Zaman lafiya ya dawo kauyen.

Bayan haka mukaddashin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya umurci sifeton ‘yan sanda da a tura karin jami’an tsaro yankin kudancin Kaduna din domin samar da tsaro. Sannan ya mika jajensa ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu da kuma fatan Allah ya ba wadanda suka sami raunuka sauki.

Share.

game da Author