Ofishin Majalisar Dinkin Duniya mai kuma da Afrika ta Yamma da Yankin Sahel, ya yaba wa Shugaban Riko, Yemi Osinbajo, bisa yadda ya shawo kan rikicin da ya afku kwanan nan a Yankin Bakassi, inda aka kashe wasu dimbin masunta ‘yan Najeriya.
Wakilin Babban Sakataren Majalisar mai kula da Afrika ta Yamma, Mohammed Chambas ne ya bayyana haka yayin da ya ke hira da wakilin kamfanin dillancin labarai a birnin New York, Amurka.
Chambas ya ji takaicin yadda Jandarman na Kamaru su ka karkashe wasu masunta ‘yan Nijeriya har 97 a yankin Bakassi, saboda sun ki biyan naira dubu dari daya a matsayin kudin harajin kwale-kwale.
Daga nan kuma ya yabi Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta NEMA, inda sake cewa ya kamata a kara bincike domin a tantance mutane nawa ne su ka tsallaka Bakassi daga Nijeriya, sannan kuma a gano wadanda ke bukatar tallafi ko agaji, musamman wadanda suka rasa muhallin su.
‘’A yanzun nan da na ke magana da ku, wata tawaga daga ofishi na ta bar Abuja inda su ka tuntubi ma’aikatar shari’a. yanzu sun zarce zuwa Kameru, inda za su sauka Yaounde domin nazarin matsolin da su ka haddasa mummunan lamarin.
“Amma dai ya zuwa yanzu, abin da mu ka samu labari shi ne rigimar ta taso ne sanadiyyar tilasta wa al’ummar wani yanki na masunta biyan wasu kudade na haraji.