Kadan ya rage marigayi Maitama Sule ya zama shugaban Najeriya. Cikin 1976 ya zama kwamishinan tarayya na ji da karbar koke-koke. Sai kuma a 1979, inda ya tsaya takarar fidda-gwanin jam’iyyar NPN a zaben shugaban kasa, inda ya fafata da Shehu Shagari a gangamin jam’iyyar a Lagos. Daga nan kuma sai aka nada shi jakada na dindindin a Majalisar Dinkin Duniya a cikin waccan shekarar. A lokacin da ya ke aikin jakadanci a Majalisar Dinkin Duniya, Maitama Sule ya rike mukamin shugabancin kwamiti na musamman a kan yaki da wariyar launin fata da Afrika ta yi fama da shi kafin ta samu ‘yanci.
Murda-murda da tuggun ‘yan siyasa ne ya hana a tsaida shi takara a taron NPN na zaben fidda gwani a Lagos cikin 1978. Kada a manta dukkan ‘yan takarar biyu sun rike mukaman ministoci a Jamhuriya ta farko, lokacin mulkin Tafawa Balewa.
A wancan lokacin, gaggan NPN sun fi karkata a kan Maitama, saboda ana kallon ya fi wayewa kuma ya fi Shagari kurda-kurda nesa ba kusa ba. Hakan ne ya sa ya samu magoya baya sosai a lokacin zaben fidda-gwanin.
Yayin da ya ja hankalin wakilai masu zabe wajen furta kalamai masu ratsa jiki wadanda ya kware da su, ga shi kuma dama ya yi shahara sosai wajen iya ado na suturar alfarma, a gefe daya kuma sai manyan ‘yan gaje-ganin jam’iyyar NPN suka kife masa baya, saboda su na tsoron idan ya zama shugaban kasa ba za su iya tankwasa shi ba.
Wani masanin tarihi Farfesa Dahiru Yahaya ya bayyana abin da ya faru a wurin zaben wanda ya ce a kan idon sa aka yi komai, domin a lokacin shi ne sakataren jam’iyyar na jiharv Kano. Dahiru ya ce makarkashiya aka yi wa Maitama tare da tuggu, abin takaici kuma da hadin bakin mutanen sa Kanawan da suka je wurin zaben.
Yayin da aka ga cewa tabbas fa Maitama ne zai lashe zabe a lokacin da aka tafi zagayen zabe na biyu, sai wasu ‘yan tuggun siyasa suka rika bi daki-dakin da kowane wakili ya ke, sun a raba kudi su na cewa “Maitama y ace ya na godiya da goyon bayan da ku ka nuna masa, amma ya ce gobe ku zabi Shagari.” Haka Farfesa Dahiru ya tuna cewa ta faru a wurin zaben.
Washegari aka yi zabe, Shagari ya yi nasara, sannan da aka yi zaben shugaban kasa kuma ya kayar da marigayi Cif Owolowo na UPN, Cif Azikwe na NPP marigayi Waziri Ibrahim na GNPP sai kuma marigayi Malam Aminu Kano na PRP.
Domin a kashe kaifin siyasar sa ne a Najeriya aka ce an ba Shagari shawarar ya samar wa Maitama wani aiki a kasar waje, yadda zai yi nisa da Najeriya. Dalili kenan aka nada shi wakilin Nijeriya a Majalisar Dinkin Duniya.
Yadda bawan Madakin Kano ya haifi Maitama Sule
Maitama Sule ya tashi a matsayin dan bawan da ya yi bauta a fadar Madakin Sarkin Kano, amma ya yi sa’ar shiga makarantar ilmin zamani har ya zama ministan da ya fi sauran ministoci dadewa a kan mulki a zamanin shugabancin Tafawa Balewa, kuma dan gaban-goshin Firayi Minista din.
Dama kuma su biyun kusan jirgi daya ya kwaso su. Yayin da mahaifin Tafawa Balewa bawan Madakin Bauchi ne, shi kuma mahaifin Maitama bawan Madakin Kano Muhmudu ne. Tarihi ya tabbatar da cewa mahaifin Maitama ya samu sunan sa Sule ne saboda sunan mahaifin Madakin Kano Mahmudu kenan.
Shi kan sa Maitama ya sha bayyanawa a wurin taruka cewa ilmin zamani ne ya kai shi matsayin da ya ke har ya ke hada kafada-da-kafada da sarakuna, maimakon ya rika bauta musu.
Madakin Kano Mahmudu ne ya tsaya-tsayin daka domin tabbatar da Maitama ya yi karatu, inda ya saka shi a Elementare ta Shahuci, a cikin 1937, daga nan kuma ya wuce makarantar Middle ta Kano, sai kuma Kaduna Kwaleji, wato Kwalejin Barewa ta yanzu.
Maitama ya koyar a Makarantar Middle ta Kano, kuma ya taka rawa wajen shiga garuruwa tare da Sarkin Kano Sanusi I ana fadakar da jama’a dangane da kiwon lafiya, ilmi da kuma haraji.
Saboda tsananin ilmin sa da kuma sanin da ya yi wajihar Kano da masarautar ta ne ya sa aka nada shi Danmasanin Kano.
Shi ne Ministan Man Ferur, tama da makamashi na farko a Najeriya, cikin 1954 a lokacin ya na da shekaru 29. Shi ne ma ya fara sanya hannu a yarjejeniya da kamfanin Shell domin su fara hakar danyen man fetur a Najeriya.
Ashafa Murnai ne ya fassara wannan Labari. Karanta a shafinmu na Turanci: OBITUARY: Maitama Sule: A servant’s son who almost became Nigeria’s president