Likitan da ya kara ma wani yaro jinin dake dauke da kwayar cutar Kanjamau zai fuskanci horo

0

Hukumar tsaro na Civil Defence a jihar Nasarawa ta kama wani likita dake duba marasa lafiya ba tare da izinin yin hakan ba.

Hukumar ta ce ta kama likitan mai suna Jonathan Ibrahim ranar 17 ga watan Yuli da laifin kara ma wani yaro dan shekara shida jinin dake dauke da cutar kanjamau a asibitin da ya bude ba tare da izini ba a shekara bara.

Shugaban hukumar NSCDC na jihar Nasarawa Lawan Bashir-Kano ya sanar da hakan wa manema labarai ranar Laraba.

Lawan Bashir-Kano ya kara da cewa sun kama Jonathan Ibrahim ne bayan karan da mutanen garin su ka kai ofishin su kan munanan aiyukkan da yake ta aikatawa a asibitin.

Da yake amsa laifin sa Jonathan Ibrahim ya tabbatar da cewa ba shi da wata masaniya kan aikin likitanci domin horar aikin duba gari ne ya samu daga jami’ar fasaha da ke Keffi.

Ya kuma ce shine ya kara wa wannan yaro jini ba tare da ya tabbatar da ingancin jinin ba a shekarar bara.

Bashir-Kano ya ce ma’aikatar kiwon kafiya tare da kungiyar likitocin hakora na kasa za su tabbatar da cewa an horar da shi bisa ga laifin da ya aikata.

Ya kuma shawarci mutane garin da su kai karan duk mutumin da suka ga yana aikata irin hakan ga jami’an tsaro.

Share.

game da Author