Kwalera: Mutane 17 sun rasa rayukansu a jihar Kwara

0

Akalla mutane 17 ne suka rasa rayukansu a jihar Kwara zuwa yanzu tun bayan barkewar cutar kwalera a a jihar.

Bayanai sun nuna cewa yara ‘yan kasa da shekaru 5 ne suka fi kamuwa da cutar da rasa rayukan su.

Bayan haka kuma wata kungiya mai zaman kanta ‘yar kasar Canada mai suna ‘Global Affairs Canada GAC ta yi kira ga gwamnatin Najeriya da ta samar da isassun magungunar da ke dauke da sinadarin Zinc and Low-osmolarity (Lo-ORS) a asibitocin gwamnati domin kawar da cutar amai da zawon yara kanana.

Kungiyar GAC ta tallafa wa fannin kiwon lafiyar Najeriya da wadannan magungunan ne a shirin ta da take kira ‘Clinton Access Health Initiative (CHAI)’ domin magance wannan annoba dake kawo ajalin jarirai da yara kanana a kasar.

Kungiyar GAC ta ce tallafin CHAI din wanda zai kare aiki a watan Yuli ta fi bada karfi wajen tallafa wa jihohin kasar da suka fi fama da wannan cutar kamar Bauchi, Cross River, Kaduna, Katsina, Niger, Kano, Lagos da Rivers.

Bincike ya nuna cewa yara 100,000 ne suka rasa rayukansu a shekaran 2012 domin karancin magungunan da ya kamata da tsadar da su ke da shi.

Wata jami’ar kungiyar Linda Erhlich ta ce a yanzu haka an sami raguwar mutuwar yara kanana domin shirin ya taimaka wajen samar da magungunan da asibitocin kasar ke bukata.

Ta kuma shawarci gwamnati da ta ci gaba da wadata asibitocin da irin wadannan magunguna musamman ga yara ganin cewa shirin bada tallafin ya kawo karshe a Najeriya.

Shugaban hukumar kula da cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko NPHCDA Faisal Shuaib ya mika godiyarsa ta musamman ga kungiyar sannan ya ce hukumarsa na nan akan bakar ta na ganin an kawar da cutar shan Inna, samar da alluran rigakafin cututtuka da gyara cibiyoyin kiwon lafiya a kasar.

Daga karshe jami’in kula da kiwon lafiyar jama’a wanda ya wakilci gwamnan jihar Kaduna Addo Mohammed ya tabbatar wa kungiyar cewa jihar Kaduna na iya kokarin ta domin ganin cewa asibitoci da cibiyoyin kiwon lafiyar a jihar na ci gaba da samun magungunan amai da zawo na yara kanana bayan tallafin ya kare.

Share.

game da Author