Hukumar Kididdigar Yalwar Arziki da Tsadar Rayuwa, ta bayyana cewa watanni biyar kenan a jere da fara samun saukin kuncin rayuwar da al’ummar Najeriya ta afka.
Hukumar ta yi wannan tambihin ne ranar Litinin, inda ta ce an samu rangwamen tsadar rayuwa a cikin watan Yuni inda malejin kunci da fatara ya yi kasa zuwa kashi 16.10 cikin 100, sabanin cikin watan Mayu, lokacin da ya kai 16.25 bisa 100.
“Wannan kididdiga na nuna cewa watanni biyar kenan a jere tsadar rayuwa na rage munana a kowane wata sai gejin talauci ke raguwa a cikin al’umma.”