Matashiyar yarinyar nan mai fafutikar kare hakkin mata, Malala Yousafzai, ta ziyarci mukaddashin shugaban kasa Yemi Osinbajo yau a Abuja ranar Litini.
Malala ta ziyarci Osinbajo ne tare da mahaifinta Ziauddin Yousafzai.
Da take ganawa da mukaddashin Shugaban Kasa Malala ta yi kira ga gwamnati da ta kara ba ilimin mata mahimmanci a kasar.
Bayan haka Malala ta ce zata ci gaba da kira ga gwamnatocin kasashe da su baiwa ilimin mata mahimmanci musamman ganin ba da dadewa bane ta kammala karatunta na sakandare.
Ta ce zata yi amfani da shafunan sada zumuntarta na yanar gizo domin ci gaba da kira kan haka.