Kotun Daukaka kara ta jaddada hukuncin daurin ‘yan Filifin 5 da Bangladesh 4

0

Ranar Litinin ne Babbar Kotun Daukaka Kara a Abuja ta jaddada hukuncin daurin wasu ‘yan kasar waje 9 da su ka hada da Fililin su 5 da kuma wasu ‘yan kasar Bangladesh su 4.

An dai yanke wa kowanen su hukuncin daurin shekaru biyar ne, bayan an same su da laifin satar danyen man fetur daga Najeriya.

Wadanda aka yanke wa hukuncin sun hada da: Axel Jabone, Zahirul Islam, Juanito Infantado, Saurin Alave da kuma Gatila Gadayan. Saurn sun hada da Islam Shahinul, Islam Rafiqul, Shaikh Nomany da Rolando Comendador.

Dukkakn su hukumar EFCC ce ta kama su, kuma ta tuhume su da laifin harkallar danyen man fetur ta haramtacciyar hanya.

Alkalan Kotun Daukaka Kara su uku da su ka hada da Mai Shari’a Hussein Mukhtar, M. L. Shuaib da Fredirick Oho ne su ka kori wannan kara da wadanda ake tuhumar su ka daukaka, a bisa hujjar cewa ba su da wata hujjar daukaka karar.

Share.

game da Author