Kotu tayi watsi da karar wanda ya saka wa karensa suna Buhari

0

Kotu dake zama a garin Sango-Ota jihar Ogun ta yi watsi da wata kara da aka shigar a gabanta kan wani mutum da ya saka wa karensa suna Buhari.

Alkalin Kotun OO Adeboh ya ce wanda ya shigar da karar Halliru Umaru bai wadata kotun da isassun bayanan da ya nuna cewa Joachim Iroko na da laifi ba kan abin da yayi.

Halliru Umaru makwabcin Joachim Iroko ne a garin Sango Ota Jihar Ogun ya maka shi a kotu ne ya na tuhumarsa kan sunan da ya sa wa karensa. Ya ce saka wa karensa suna Buhari cin fuska ne kuma hakan bai kamata ba.

Joachin Iroko dai ya saka wa karensa suna Buhari tun shekarar bara, dalilin haka ya sa Halliru ya maka shi a kotu.

Share.

game da Author