Kira ga gwamnati da ta samar da Allurar Rigakafi ga Mutane

0

Shugaban kungiyar ‘Health Sector Reform Coalition’, HSRC, Ben Anyene ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta samar da isassun kudaden da ake bukata wajen samar da alluran rigakafi a Najeriya.

Ya ce ya yi wannan kira ne ganin cewa kungiyar GAVI zata janye tallafin da take ba Najeriya gudun kada a shiga Matsanancin hali.

Ya ce kamata yayi Najeriya ta fara ware wasu kudede domin wadatar da irin wadannan allurai ba sai sun tafi ba ya zama matsala.

Ya ce jihohin kasa za su iya ware biliyan biyu kowace shekara domin kiwon lafiyar mutanen su sannan gwamnatin tarayya ta cikasa sauran kudin.

Share.

game da Author