Kira ga gwamnati da ta halasta sana’ar mu – Karuwan Najeriya

0

Shugaban kungiyar karuwai na Najeriya Amaka Anemo ta yi kira ga gwamnati da ta halasta sana’arsu domin hakan zai taimaka wajen rage yaduwar cutar kanjamau da cin mutuncinsu da wasu kwastamomi ke yi.

Amaka Anemo ta ce munafunci na daya daga cikin dalilan da ka iya hana gwamnati biya musu bukatunsu. Misali mafi yawa yawan mutanen da suke tir da sana’ar da suke yi ke dawo daga baya a boye domin su sami biyan bukatar su sannan kuma garin yin hakan su ci mutuncin karuwan daga baya.

Ta ce ta yi wannan kira ne saboda sakamakon binciken da cibiyar kula da kiwon lafiyar jama’a na jami’ar Manitoba dake kasar Canada da hukumar kula da hana yaduwar cutar kanjamau na kasa NACA suka fitar.

Sakamakon binciken ya nuna matsalolin da sana’ar karuwanci ke tattare da shi wanda ya hada da kamuwa da cututtuka musamman kanjamau, yada cututtuka, cin mutuncinsu da wasu kwastamomi da jami’an tsaro kan yi, rashin samun ingantaciyyar kula a asibitoci da sauran su.

Daga karshe ta ce yin hakan kadai ne zai taimaka musu wajen samun kariya da kiwon lafiyar da suke bukata.

Share.

game da Author