Kasar saudiyya da na Iran sun warware takaddamar da ke tsakaninsu da ya sa kasar Saudiyya ta dakatar da kasar Iran daga zuwa aikin Hajji a shekarar da ta gabata.
Hakan dai ya samo daliline tun bayan mutuwar da mutane suka yi a wajen jifa a shekarar 2015.
Shugaban hukumar kula da jin dadin Alhazai na kasar Iran Ali Askar ya tabbatar da wannan ganawa da kasashen biyu suka yi.