Shugaban hukumar kula da hana yaduwar cutar kanjamau Sani Aliyu ya ce gwamnonin jihohin Najeriya sun amince su ware kashi 0.5 zuwa kashi daya bisa 100 na kudaden da suke samu a jihohin don samarda kula ga mutanen dake dauke da cutar kanjamau.
Ya fadin haka ne ranar Lahadi da yake zantawa da manema labarai a Abuja.
Sani Aliyu ya ce wannan kudi da za su ware zai taimaka wajen ganin kashi 90 bisa 100 na mutanen da ke dauke da cutar kanjamau na samun kular da ya kamata wanda ya hada da karban magungunan da zai hana yaduwar cutar.
Sani Aliyu ya kara da cewa kudaden zai taimaka wajen samar da magunguna ga mutanen da ke dauke da cutar wanda hakan zai rage yadauwar cutar a kasan.
‘’Idan sama da kashi 80 bisa 100 na mutanen da ke dauke da cutar na samun maganin cutar zai taimaka wajen kawar da cutar da yaduwar ta.
Bayan haka Sani Aliyu ya ce gwamnatocin jihohin sun amince su samar da kula wa mata masu ciki da ke dauke da cutar kanjamau kyauta a asibitocin jihohin.
Ya ce kudin da mace mai ciki wace take dauke da cutar zata bukata ya kai Naira 50,000 wanda a ganin sa Najeriya za ta iya biyan wannan kudi.
Ya kuma yi kira ga gwamnatin jihohin kasar da su saka yin gwaji da samun kula ga masu dauke da cutar kanjamau cikin shirin inshorar kiwon lafiya domin hakan zai taimaka wajen samar wa mutane da daman samun magani sannan kuma da hana yaduwar cutar.
Discussion about this post